NE

News Elementor

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, Ya Amince Da a Biya Ma’aikata Albashin Watan Fabrairu

A wani yunkuri na ganin an saukakawa ma’aikatan Jihar nan,domin su fara azumin watan Ramadan mai alfarma na bana cikin walwala, Mai Girma Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, PhD, FCNA, ya amince da biyan albashin watan Fabrairu nan take, wanda zai fara daga gobe Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026.

Kamar yadda aka saba, biyan albashin ya shafi ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Kananan Hukumomi, ma’aikatan Hukumar Ilimi ta Kananan Hukumomi (LGEA), da kuma tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a faɗin jihar.

A bisa ga haka,Gwamnan jiha Ahmed Aliyu Sokoto, ya bukaci ma’aikatan gwamnati da su sakawa wannan karamci da sauran alheran da gwamnatin jiha ke yi musu, ta hanyar nuna ƙwazo da jajircewa wajen aiwatar da ayyukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM