
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai kai ziyarar aiki ta rana ɗaya a Jihar Kebbi ranar Asabar domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.
A wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, an bayyana cewa shugaban zai ƙaddamar da ayyukan da gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris, ya gudanar.
Yayin ziyarar tasa, Shugaba Tinubu zai kasance babban baƙo na musamman a bikin kamun kifi na Argungu International Fishing and Cultural Festival karo na 61 na shekarar 2026.
Bikin, wanda ke daga cikin manyan bukukuwan al’adu da aka fi sani da su a Afirka, ana shirya shi ne a bakin kogin Matan Fada mai tarihi.
Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNESCO, ta amince da bikin a matsayin gadon al’adu l na bil’adama.
Sanarwar ta fito ne ta hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai , Bayo Onanuga, a ranar Juma’a.