NE

News Elementor

Mulkin Kano ba abu ne mai sauƙi ba -Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gudanar da mulkin jihar ba abu ne mai sauƙi ba, inda ya bayyana Kano a matsayin ƙaramar Najeriya saboda yawan al’ummarta da kuma yanayin zamantakewarta da ya ƙunshi mutane daga sassa daban-daban.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ambasada Ibrahim Waiya, wanda ya wakilce shi a taron tsaro na farko na shekara-shekara na Cibiyar Nazari da Dabarun Tsaro (ISSS), inda aka karrama shi da lambar yabo ta ƙwarewa wajen gudanar da harkokin tsaro.

Taken taron shi ne “Gina Tsarin Tsaron Ƙasa Mai Juriya: Ƙirƙire-ƙirƙire, Bayanai da Haɗin Kan Al’umma Domin Samar da Najeriya Mai Ingantaccen Tsaro”.

Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabon, Waiya ya ce karramawar ta zama wani ƙarin kira ga gwamnati da ta ƙara himma wajen gudanar da harkokin tsaro, yana mai cewa gwamnatin jihar ta rungumi hanyoyin da suka haɗa da matakan amfani da ƙarfi da kuma waɗanda ba na ƙarfi ba wajen yaƙi da rashin tsaro.

Ya ce gwamnatin ta horas da kusan matasa maza da mata 2,000 ƙarƙashin shirin Neighbourhood Watch, sannan ta tura su zuwa ƙananan hukumomi 44 domin su taimaka wa hukumomin tsaro na yau da kullum.

Ya kuma bayyana matakan da suka haɗa da Anti-Phone Snatching Corps, wato rundunar yaƙi da satar wayoyin hannu, da kuma shirin Safe Corridor, wanda ya ce an ƙirƙire shi ne domin ƙarfafa matasan da ke da hannu wajen daba da tashe-tashen hankula na siyasa su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.

A cewarsa, an yi wa matasa maza kusan 340 rajista tare da tantance su ƙarƙashin shirin Safe Corridor, yayin da gwamnatin ta fitar da sama da naira miliyan 500 domin gudanar da shirin.

Da yake magana kan ƙalubalen mulki, Yusuf ya ce: “Kamar yadda ɗaya daga cikin masu gabatar da jawabi a taron ya faɗa, mulki ba abu ne mai sauƙi ba. Ba aikin malalaci ba ne, domin a zahiri kana mulkin jiha ce da take kamar ƙaramar Najeriya.

“Kano na da yawan al’umma sosai, kuma a baya-bayan nan an bayyana ta cikin biranen da suka fi yawan jama’a a duniya. Jiha ce mai cike da mutane daga sassa daban-daban, kuma ta zama matattarar ‘yan Najeriya, saboda mutane daga kusan dukkanin sassan Najeriya suna zaune a Kano.

“Saboda haka, Kano a zahiri ƙaramar Najeriya ce, kuma mulkinta ba abu ne mai sauƙi ba,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM