NE

News Elementor

Kotu ta ɗage sauraron ƙarar Nafiu Bala akan Mark da Aregbesola

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da Nafiu-Bala Gombe ya shigar, wadda ya ke neman a hana shugabannin ADC da David Mark ke jagoranta, ci gaba da gabatar da kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar, zuwa ranar 28 ga watan Satumba.

An sanya ranar Litinin domin sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen da ke gaban kotun dangane da ƙarar, sai dai zaman bai yiwu ba saboda Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Peter Lifu, bai zauna ba.

Daga bisani, kotun ta sanya ranar 28 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraron shari’ar.

A ranar 16 ga watan Yuni, Mai Shari’a Lifu ya sanya ranar sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen da ke gaban kotun, bayan da ya yi watsi da buƙatar da aka gabatar ta neman ya janye daga shari’ar.

Alƙalin ya ce buƙatun biyu da jam’iyyar ADC da Ogbeni Rauf Aregbesola, waɗanda suke a matsayin wanda aka ƙara na farko da na uku, suka gabatar, ba su da hujjar da za ta sa a amince da su.

Saboda haka, ya ci tarar ADC da Aregbesola Naira miliyan ɗaya kowannensu, inda kuɗin za su tafi ga Nafiu-Bala Gombe.

ADC da Aregbesola sun gabatar da buƙatu daban-daban ga Mai Shari’a Lifu, suna neman ya janye daga sauraron ƙarar da Gombe ya shigar, bisa zargin cewa yana nuna son kai a shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM