Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe naira biliyan 1.759 domin sayen babura kirar Bajaj guda 1,000 da za a bai wa hukumomin tsaro domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga a jihar.
An cimma matsayar ne a taron majalisar zartarwar jihar karo na shida na shekarar 2026, wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Idris Muhammad Gobir, ya jagoranta.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, za a raba baburan ga hukumomin tsaro domin ƙara musu ƙarfin gudanar da ayyukan tsaro, musamman a yankunan da matsalar ’yan bindiga ta fi kamari.
Wannan amincewa ta zo ne jim kaɗan bayan da gwamnatin jihar ta sayi motocin yaƙi masu sulke guda 62 kan kuɗi naira biliyan 27, waɗanda aka raba wa hukumomin tsaro domin inganta ayyukan tsaro a faɗin jihar.
Baya ga batun tsaro, majalisar ta amince da wasu ayyuka da suka shafi ilimi, lafiya, samar da ruwa da koyar da sana’o’i.
Daga cikin ayyukan akwai amincewa da kashe naira miliyan 723.17 domin gyaran makarantar Government Technical College da ke Runjin Sambo, da kuma naira miliyan 498.99 domin gyarawa da sake fasalin makarantar A.A. Raji Special School.
Haka kuma, majalisar ta amince da kashe naira miliyan 489.31 domin gyaran kashi na farko na kwalejin Kimiyyar aikin jinya, yayin da aka ware naira miliyan 229.36 domin gyaran dakunan kwanan ɗalibai na maza da mata a Kwalejin Basic and Remedial Studies.
Majalisar ta kuma amince da naira miliyan 174.64 domin gyaran gidajen ma’aikata da inganta katangar kwalejin aikin gona da kimiyyar dabbobi da ke Wurno.
Haka zalika, an amince da naira miliyan 133.66 domin gina katanga a cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Wamakko, da kuma naira miliyan 93.88 domin sayen kayan koyar da sana’o’i ga cibiyoyin koyar da sana’o’in mata guda 46 da ke faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Bugu da ƙari, majalisar ta amince da kashe naira miliyan 90.20 domin sayen bututun PVC da kayan aikin famfo da za a yi amfani da su wajen kula da tsarin samar da ruwan sha na birane guda 142 a ƙananan hukumomi 23 na jihar.