Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa a shirye take ta sasanta da tsohon gwamnan jihar kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bayan tsohon gwamnan ya ce kofarsa a bude take domin sulhu da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Ibrahim Waiya, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 20 ga Satumba, yayin wata tattaunawar waya da jaridar Leadership.
Waiya ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf tana kallon Kwankwaso a matsayin uba, saboda haka ba za ta yi watsi da duk wani yunkuri na dawo da kyakkyawar alaka tsakaninsu ba.
A cewarsa, kamar yadda Kwankwaso ya bayyana cewa kofarsa a bude take ga sulhu, gwamnatin Kano ma a shirye take ta karbi irin wannan yunkuri.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Yusuf ya taba jan hankalin magoya bayansa da kada su dauki Kwankwaso a matsayin abokin gaba, saboda matsayin da yake da shi a gare su.
Waiya ya ce abin da ya faru tsakanin bangarorin ba wai yaki ba ne, illa dai bambancin ra’ayi da ya taso a siyasa.
Wannan bayani na gwamnatin Kano ya zo ne kwana guda bayan Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu yana kaunar Gwamna Abba Yusuf, tare da cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya hana sulhu ba.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa da aka wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce bai yi watsi da Abba ba, kuma bai taba neman ya bar tafiyar siyasa ba.