NE

News Elementor

Gwamnatin Kano Za Ta Ɗauki Sababbin Malamai 4,000

Shugaban Hukumar Kula da Ilimin bai-ɗaya ta Jihar Kano SUBEB, Yusuf Kabir, ya ce hukumar na shirin ɗaukar karin malamai 4,000 domin inganta karatu da ilimin lissafi a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Ya bayyana hakan ne a lokacin taron nazarin sakamakon koyo na kwata na shekarar 2025, wanda aka shirya domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan cigaban ƙwazon ɗalibai a karkashin shirin shekaru uku na (Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE), wanda gwamnatin Birtaniya ke ɗaukar nauyi.

Kabir, wanda Sakatariyar Hukumars, Hajiya Amina Umar, ta wakilta, ya ce ko da yake an dauki malamai 4,343 a ɗaukar ma’aikata na baya-bayan nan, jihar har yanzu na fama da karancin malamai.

“Muna da bukatar karin malamai 4,000, kuma da dama sun nuna sha’awar neman aikin. Mun riga mun fara shirya cibiyoyin CBT guda bakwai a Wudil, Bichi, da wasu wurare domin gudanar da jarrabawar cancanta,” in ji shi.

A cikin sauye-sauyen da ake shirin yi, jihar na neman rage yawan cinkoson dalibai 132 da malami ɗaya ke kula da su—zuwa malami daya kan dalibai 60.

Wani mai ruwa da tsaki, Dr. Miswaru Bello, ya bayyana damuwa cewa kashi 40% na daliban Kano ba sa zuwa makaranta, sannan rashin zuwa aiki daga malamai ya kai kusan kashi 12%.

Taron ya ba da shawarar fadada zangon koyon gaggawa na lokacin hutu da ƙarfafa horaswa ga malamai a makarantu, da inganta sa ido kan halartar malamai da dalibai a makarantu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM