NE

News Elementor

Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na ƙara ta’azzarar rashin tsaro da almundahanar kuɗi – Majalisar wakilai

Kwamitin wucin gadi na Majalisar wakilai mai bincike kan haƙar ma’adinai, tsaro da yaƙi da almundahanar kuɗi ya bayyana cewa haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na ƙara ta’azzarar rashin tsaro, almundahanar kuɗi da kuma rage wa gwamnati kuɗaɗen shiga.

Shugaban kwamitin, Sani Abdulraheem, ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan inganta tsarin tafiyar da harkokin ma’adinai da aka gudanar a Abuja.

Ya ce ƙungiyoyin masu aikata laifuka na cin gajiyar raunin dokoki da rashin ingantaccen sa ido wajen satar albarkatun ma’adinai, lamarin da ke hana Najeriya amfana da dimbin arzikin da take da shi.

Abdulraheem ya ce kwamitin ya fara bincike kan girman matsalar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, hanyoyin da ake amfani da su wajen halasta kuɗaɗen haram da kuma tsarin tsaron yankunan da ake haƙar ma’adinai.

Ya kuma buƙaci hukumomin tsaro, masu yaƙi da cin hanci, ma’aikatar ma’adinai, gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin kawo ƙarshen matsalar, yana mai tabbatar da cewa binciken ba zai hana masu lasisin haƙar ma’adinai gudanar da halastattun ayyukansu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM