Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa hukuncin Kotun daukaka kara kan rikicin shugabancin jam’iyyar bai soke zaben fidda gwani na ADC domin babban zaben 2027 ba.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce hukuncin kotun ya shafi zabukan shugabancin jihohi da wa’adin kwamitocin zartarwa na jihohi kawai, ba zabukan fidda gwani da aka gudanar karkashin dokar zabe ba.
Ya zargi wasu da karkatar da ma’anar hukuncin domin yaudarar jama’a da raunana ‘yan adawa, yana mai cewa jam’iyyar za ta daukaka kara zuwa Kotun Koli domin neman hukunci na karshe.
Atiku ya kuma bukaci mambobin ADC su ci gaba da hada kan su tare da shirye-shiryen babban zaben 2027, yana mai jaddada cewa burin jam’iyyar na kawo sauyi a Najeriya bai canza ba.