
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Kare Kasuwanni da Kwastomomi FCCPC da ta binciki manyan kamfanonin fasaha na duniya da kuma kamfanonin AI kan zargin amfani da labaran kafafen yaɗa labaran Nijeriya ba tare da izini ko biyan kuɗi ba.
Matakin ya biyo bayan wani ƙorafi da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya suka kai wa fadar shugaban ƙasa, ciki har da NPAN, NUJ, BON da Guild of Corporate Online Publishers.
Umarnin ya fito ne ta hannun Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, wanda ya aika da saƙon ga hukumar FCCPC domin ta fara bincike