NE

News Elementor

Iconic Digital Media Tasamu Lasisi Daga Hukumar ARCON Ta Kasa

Gwamnatin Tarayyar ta hannun hukumar kula da tallace-tallace ta ƙasa (ARCON), ta bai wa kamfanin Iconic Digital Media Services Limited cikakken lasisin gudanar da harkokin tallace-tallace a faɗin ƙasar nan.

Babban daraktan kamfanin, Dr. Anas Sanusi Gusau ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook, inda ya bayyana amincewar a matsayin wani babban cigaba da nasara ga kamfanin Iconic Digital Media.

A cewarsa, lasisin ya bai wa kamfanin damar gudanar da ayyukan tallace-tallace a dukkan jihohin Najeriya, alamar shirinsa na yin aiki a matakin ƙasa baki ɗaya.

Dr. Gusau ya ƙara da cewa amincewar da aka ba su wata shaida ce ta ƙwarewa da bin ƙa’idojin hukumomi, yana mai tabbatar da cewa kamfanin ya shirya tsaf domin yi wa abokan hulɗa ingantacce kuma karɓaɓɓen aiki daga hedikwatarsa da ke birnin Lagos.

Ya kuma miƙa godiya ga hukumomin da abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka bayar, tare da alƙawarin gabatar da ingantattun, sabbin dabaru da kuma tallace-tallace dake bin ƙa’ida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM