NE

News Elementor

Jagoran Jam’iyyar (NDC) Sanata Seriake Dickson, ya bayyana jam’iyyarsa a matsayin jam’iyyar adawa mafi girma a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dickson ya ce wannan ne karo na farko da zai koma Jihar Bayelsa tun bayan da ya kafa jam’iyyar NDC tare da gina ta da kuma kafa mata tubali.

Ya gode wa ’yan Najeriya, ’yan takarar jam’iyyar da kuma abokan hulɗa, musamman ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi da mataimakinsa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya ce: “A yau, ta zama babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa a cikin ƙasar nan.

Dickson ya jaddada cewa dole ne dimokuraɗiyya da tsarin jam’iyyu masu yawa a Najeriya su dore.

Ya ce a halin yanzu jam’iyyar na fuskantar abin da ya kira “dabarun shari’a da aka ƙirƙira na wasu masu adawa da dimokuraɗiyya, inda ya kara da cewa wannan ma zai wuce.

Sanata Dickson bayyana kwarin gwiwarsa cewa bangaren shari’a zai yi aiki bisa doka, kuma ba zai bari a yi amfani da shi a matsayin wata hanya ta kawo cikas ga dimokuraɗiyya ba.

Ya kuma yi nuni da wasu mutane da ya ce ya taimaka wajen tasowa tare da tallafa musu tsawon shekaru, waɗanda ya zarge su da juya baya tare da fara amfani da hukumomin gwamnati wajen korar mutane daga mukamai, gallaza wa ’yan ƙasa marasa laifi, yaɗa farfaganda maras tushe, da mayar da alherin da aka yi musu a baya da “mugunta da sharri”.

Ya yi kira ga jama’a su shirya domin gudanar da siyasar da ba ta da tashin hankali ba, siyasar tunani da manufofi,” wadda ya ce shi ne ya ci gaba da jagoranta a duk tsawon rayuwarsa ta siyasa.

Dickson ya yi gargadi ga waɗanda manufarsu ita ce barazana da tsoratar da jama’a, amfani da hukumomin gwamnati wajen yaƙar mutanen ƙasarsu, da kuma haddasa tashin hankali a tsakanin al’umma, inda ya ce za a sake kunyata su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM