NE

News Elementor

Dunald Trump ya ce dole ne Saudiyya ta amince da Isra’ila kafin su ƙulla yarjejeniyar nukiliya

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yarjejeniyar nukiliya tsakanin ƙasarsa da Saudiyya za ta fara aiki ne kawai idan Saudiyyar ta amince da shiga yarjejeniyar Abraham da aka fi sani da fi sani da Abraham Accords, wadda ke nufin amincewa da gwamnatin Isra’ila a hukumance.

A baya-bayan ne dai Amurka da Saudiyya suka amince da ƙulla yarjejeniyar samar da nukiliya na zaman lafiya ga Saudiyya.

To sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce ”Za a amince da Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Fasahar Nukiliya ta Farar Hula, wadda ta taƙaita ne ga amfani da makamashin nukiliya ba don harkokin soja ba, amma hakan ya dogara ne da shigar Saudiyya Yarjejenar Abraham”.

Sharaɗin na Trump na zuwa ne bayan da masana suka yi gargaɗin cewa yarjejeniyar za ta iya ƙara hatsarin bazuwar makaman nukiliya a yankin Gabas ta Tsakiya da ke fama da rikice-rikice”.

Batun nukiliya na daga cikin abubuwan da suka jima suna haɗa Amurka da Isra’ila faɗa da Iran.

A 2020, Shugaba Trump ya samu nasarar cimma yarjejeniyar Abraham, wadda ta sa ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahraine suka kyautata alaƙar diplomasiyyarsu da Isra’ila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM