NE

News Elementor

Jigo a jam’iyyar NDC Pat Utomi ya ce idan Obi ya ci zabe zai daidaita farashin Dala zuwa N500

Masanin tattalin arziki kuma jigo a jam’iyyar NDC, Farfesa Pat Utomi, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, zai iya rage darajar dala zuwa naira 500 tare da saukar da farashin kayan masarufi da kashi 50 cikin 100 idan ya lashe zaben 2027.

Utomi ya bayyana cewa shirin tattalin arzikin jam’iyyar zai mayar da hankali kan karfafa darajar naira, inganta tsaro, wutar lantarki da hanyoyi domin rage hauhawar farashi da talauci.

Ya ce farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 zai iya sauka daga N55,000 zuwa N27,500, yayin da litar man fetur za ta koma N500 daga N1,350.

Haka kuma, ya yi hasashen cewa buhun siminti zai sauka daga N13,500 zuwa N2,000, yayin da buhun masara zai ragu daga N75,000 zuwa N37,500.

Utomi ya ce wannan shiri zai taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya miliyan 140 da ke fama da talauci ta fuskoki daban-daban.

Sai dai bai bayyana lokacin da za a cimma wannan buri ba, ko kuma takamaiman matakan kudi da gwamnatin Obi za ta dauka domin tabbatar da hakan.

A halin yanzu, bayanan da rahoton ya kawo sun nuna cewa ana musayar dala kan kusan N1,346 a kasuwar canjin kudi ta hukuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM