Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi na Jihar Kaduna, Mukhtar Monrovia, ya ce Gwamna Uba Sani bai karɓi ko sisin kobo ba da sunan rance tun bayan hawansa karagar mulki.
Monrovia ya bayyana cewa za a aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 ba tare da karɓar bashi ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Monrovia ya ce za a samar da kuɗaɗen kasafin 2026 ne daga kason da jihar ke karɓa daga gwamnatin tarayya da kuɗaɗen shiga na cikin gida da kuma tallafi.
Ya ƙara da cewa rahotannin da ke nuna cewa jihar za ta sake karɓar rance sun samo asali ne daga rashin fahimtar batun “loan drawdown” da aka saka a cikin kasafin kuɗin.
