Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, sun kama wani mutum da ake zargin shi ne ya jagoranci harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci da ke Maidugurin Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu 34.
An sanar da kama wanda ake zargin ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar.
Ya bayyana wanda aka kama da sunan Sheriff Umar, a matsayin babban mai tsara hare-haren kunar bakin wake da ke da alaƙa da wasu hare-hare da aka kai da kuma waɗanda aka dakile a yankin Arewa maso Gabas.
A cewar sanarwar, an kama wanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike da kewaye wurare bisa sahihan bayanan sirri a unguwar Kalmari da ke Maiduguri a ranar 31 ga Disamba, 2025.
A yayin wannan aiki, an kama mutane 14 da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan kunar bakin wake.
Laftanar Kanal Uba ya ce bayan zurfafa bincike, an gano shirin ƙungiyar, rawar da kowane mutum ke takawa, da kuma alaƙar da ke tsakaninsu.
Ya ƙara da cewa wani da ake zargin ɗan kunar bakin wake ne da ke tsare a yanzu, Ibrahim Muhammad, ya bayyana Sheriff Umar, wanda aka fi sani da “Yusuf”, a matsayin shugaban ƙungiyar kuma mai kula da ayyukanta.
Binciken ya kuma nuna cewa wanda ake zargin ya shirya harin kunar bakin wake da aka kai a Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga Disamba, 2025, inda wani abokin aikinsa mai suna Adamu ya tayar da bam ɗin da ke a jikinsa tare da rasuwa a wurin.
Uba ya ce an kuma danganta wanda ake zargin da yunƙurin kai wani harin kunar bakin wake da aka dakile a Damaturu, inda ake zargin ya miƙa kayan haɗa bamabamai ga wanda aka shirya zai kai harin.
