Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama mutane biyar bisa zargin lalata allunan talla da fastocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu ’yan siyasa a jihar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida kan matakan tsaro da kuma aiwatar da dokar hana hawan doki a bainar jama’a a Kano.
Bakori ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike kan lalata kadarori a lokacin da ake samun tashe-tashen hankula da suka shafi hawan doki da jerin gwanon jama’a a jihar.
Ya ce an kammala bincike, sannan aka gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, yana mai cewa rundunar za ta ci gaba da daukar matakin doka kan duk wanda aka samu da aikata laifukan da ka iya kawo barazana ga zaman lafiyar jama’a.
Kamen ya biyo bayan wata fitowar jama’a da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya yi a ranar Lahadi.
Kwamishinan ya ce rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mutanen da suka raka sarkin sun lalata wasu fastoci da allunan talla mallakar Shugaba Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu ’yan siyasa.
Ya ce lamarin ya kara tsananta yanayin rashin jituwar da ake ciki, musamman ganin cewa har yanzu ana ci gaba da takaddamar masarautar Kano.