
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a tsare Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, a Gidan Gyaran Hali na Kuje.
Mai shari’a Mohammed Umar, a cikin gajeren hukuncin da ya yanke ranar Litinin, ya umarci a ci gaba da tsare Sowore a gidan gyaran halin har sai an saurara kuma an yanke hukunci kan ƙorafinsa na neman dakatar da umarnin soke belinsa da kuma sammacin kama shi da kotu ta bayar.
Haka kuma, Mai shari’a Umar ya yi watsi da buƙatar da Sowore ya gabatar tun da farko, wadda ke neman mai shari’ar ya janye kansa daga sauraron shari’ar bisa zargin nuna son kai