NE

News Elementor

Yan Bindiga Sun Sace Mutum 10 Da Ƙona Fadar Sarki A Jihar Kwara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane kimanin 10, ciki har da mata da kananan yara a harin da suka kai fadar Sarkin Yashikira, da ke ke Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara.

Rahotanni sun bayyana cewa a a cikin daren ranar Lahadi ne mahara dauke da muggan makamai suka kai harin, inda suka rika harbi babu kakkautawa, maharan suka kona fadar sarkin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun dauki awanni suna cin karensu babu babbaka ba tare da wata turjiya ba.

Majiyoyi sun ce bayan harin wanda ya zo wa al’ummar yankin da ba zata, jami’an tsaro sun fara aikin kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

A cewarsu, sojoji da ’yan sanda sun fara shara a dazukan da ke yankin da zummar ceto mutanen da aka sace.

Sun bayyana cewa maharan sun kai hari a ofishin ’yan sanda da ke yankin, amma jami’an da ke bakin aiki suka fatattake su, bayan musayar wuta

Wannan lamari ya faru ne washegarin da ’yan bindiga suka kai wa masu ibadar dare hari yankin Ori-Oke Ajaiye, da ke wajen kauyen Ikiran a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara, inda suka kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu 15.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM