Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a ƙarƙashin jam’iyyar NDC ba zai yi nasara a jihar Kano ba a zaɓen 2027.
Ganduje, yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, ya bayyana cewa tikitin “ya mutu tun kafin ya fara”, yana mai cewa ba su da tarihin shugabanci da ƙarfin siyasa da zai sa al’ummar Kano su amince da su.
Ya kuma tambayi irin abin da Peter Obi ya cim ma lokacin da yake gwamnan jihar Anambra, yana cewa bai nuna ƙwarewar da za ta tabbatar zai iya jagorantar Najeriya ba.
Haka kuma, Ganduje ya soki tarihin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa bai samu wa’adi biyu a jere a matsayin gwamnan Kano ba, sabanin Ibrahim Shekarau da shi kansa waɗanda suka yi shekara takwas a jere.
A cewarsa, Kwankwaso bai bar wata gagarumar gada a Kano da za ta gamsar da al’umma cewa zai iya zama mataimakin shugaban ƙasa mai nasara.