Shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa (NDLEA), Brig.-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), ya ce hukumar ta kama mutane 77,859 da ake zargi da laifukan miyagun ƙwayoyi tare da ƙwace sama da kilo miliyan 14.8 na miyagun ƙwayoyi tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
Marwa ya bayyana hakan ne a Dutse yayin bikin sanya hannu kan dokokin zartarwa da Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yi domin ƙarfafa yaƙi da shaye-shaye da wayar da kan al’umma.
Ya ce a cikin wannan lokaci, an samu hukuncin kotu kan mutane 14,122, yayin da sama da mutum 50,000 suka amfana da shawarwari da kulawar jinya a cibiyoyin gyaran masu shaye-shaye na NDLEA.
Marwa ya yabawa gwamnatin Jigawa kan matakan da take ɗauka wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai bayyana ƙaddamar da Kwamitin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi na jihar a matsayin abin koyi ga sauran jihohi.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya ce dokokin zartarwar an yi su ne domin kare makomar matasan Jigawa, tare da jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su rage shaye-shaye da inganta tarbiyyar matasa.