
Matasa a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Plateau a wannan Litinin sun toshe babbar hanyar shiga Jos domin nuna takaicinsu kan kashe-kashen da wasu ‘yan bindiga suka yi a yankin a ranar Lahadi.
Matasan, tare da mata da sauran masu goyon masu baya, sun yi fatali da duk wani kira da ake yi musu na su bar hanyar, inda suka sha alwashin za su ci gaba da zaman dirshin a wurin har sai an kama waɗanda suka kai harin tare da hukunta su bisa doka.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Samson Godiya, yana nuna takaicinsa kan lamarin.