NE

News Elementor

Mun sanya hannu kan yarjejeniyar cewa Obi wa’adi daya kacal zai yi idan ya lashe zaɓe – Kwankwaso

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabbatar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar, Peter Obi, ya sanya hannu kan yarjejeniyar yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu kacal idan ya lashe zaɓen 2027.

Kwankwaso ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce yarjejeniyar ta tanadi cewa bayan wa’adin Obi daga 2027 zuwa 2031, mulkin shugaban ƙasa zai koma yankin Arewa bisa tsarin rabon mulki da jam’iyyar ta amince da shi.

Ya ce shi da Obi sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta musamman baya ga wadda jam’iyyar ta yi, yana mai bayyana cewa yana da cikakken yaƙinin Obi zai cika alƙawarin.

Kwankwaso ya ƙara da cewa ya amince ya zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa ne saboda fahimtar cewa yankin Kudu zai riƙe mulki na wa’adi ɗaya kawai kafin a mayar da shi Arewa.

Ya kuma ce a halin yanzu jam’iyyar ta fi mayar da hankali kan lashe zaɓen 2027, yayin da take da tsare-tsaren siyasa na matsakaici da na dogon lokaci. A baya dai Peter Obi ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, zai yi wa’adi ɗaya ne kawai domin inganta zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM