Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai da rai da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru biyu, tana mai cewa hukuncin bai dace da girman laifukan da suka aikata ba.
Kotun ta yanke wa Mahmud Usman (wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas/Mukhtar), da mataimakinsa Mahmud al-Nigeri hukuncin ɗaurin rai da rai bayan sun amsa laifuka 32 da suka shafi ta’addanci.
Wani babban jami’in DSS ya ce hukumar za ta nemi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta maye gurbin hukuncin da hukuncin kisa, yana mai zargin cewa ‘yanbindigar da suka sace malamai da ɗalibai a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo sun nemi a saki waɗannan shugabannin Ansaru a matsayin sharadin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Jami’in ya ƙara da cewa an kashe malamai biyu yayin da suke hannun masu garkuwa da mutanen domin matsa wa gwamnati lamba ta saki waɗannan kwamandojin, don haka hukuncin ɗaurin rai da rai ba zai wadatar wajen tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda aka kashe ba.