Kungiyar gwamnonin arewa ta jaddada goyon bayanta kan batun kafa yansandan jihohi domin dakile matsalolin tsaro.
Shugaban kungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ne ya sanar da hakan yayin zaman kungiyar a birnin Abuja.
Gwamnan na Gombe ya ce barazanar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu na bukatar daukar mataki na musamman da zai hada da alummar yankunan da lamarin ya shafa.
Yahaya ya kuma yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a bisa kokarin da yake yi tare da majalisar tarayya domin bada damar kafa yansandan na jihohi.
Kungiyar ta kuma nanata kudurinta wajan aiwatar da asusun kula d atsrao na yankin arewa, inda kowace jiha za ta bada gudummawar naira biliyan 1 a kowane wata.
Ya yabawa jihohin Nasarawa, Gombe, Kebbi da Kaduna a bisa bayar da nasu kudin, inda ya bukaci sauran jihohin da suma su yi hakan.