NE

News Elementor

Najeriya Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tsaro Ta Shekara Biyar

Najeriya da Masarautar Saudiyya sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna ta tsawon shekaru biyar domin karfafa hadin gwiwar tsaro da na soja tsakanin kasashen biyu.

Ƙaramin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle ne ya sanar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Yarjejeniyar ta ƙunshi ƙarin hadin kai a fannin horon soja da musayar bayanan sirri da kera makaman tsaro da gudanar da ayyukan tsaro na dabaru, da sauran matakan da za su kara ƙarfafa tsaron kasa da yanki.

A cewar sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yaɗa labarai, Ahmed Dan Wudil ya fitar, wannan mataki babban ci gaba ne wajen zurfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Abuja da Riyadh.

Matawalle ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin Najeriya, yayin da Dakta Khaleed H. Al-Biyari ya wakilci gwamnatin Saudiyya.

Ma’aikatar Tsaro ta bayyana wannan ci gaba a matsayin abin da ya zo kan gaba, tare da fatan cewa hadin gwiwar zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a wasu sassan kasar.

“Wannan yarjejeniya na nuna shirye-shiryen Najeriya na yin aiki tare da abokan hulɗa na duniya domin karfafa tsaronta,” in ji sanarwar.

“Da wannan sabuwar huldar, muna da yaƙinin cewa matsalolin tsaro da ake fama da su za su ragu sosai.”

Ana sa ran yarjejeniyar ta shekaru biyar za ta kara inganta gina kwarewa, ingancin ayyukan tsaro, da aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM