Gwamnatin Najeriya ta buƙaci yanƙasarta mazauna Iran da sauran ƙasashen yankin Gulf su zama masu kula da sanya idanu sosai, bayan da yaƙi ya ɓarke a yankin.
Da safiyar yau ne Amurka da haɗin gwiwar Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare cikin Iran, yayin da ita ma Tehran ta mayar da martani da hanyar harba makamai masu linzami cikin Isra’ila da wasu sansanonin sojin Amurka a yankin Gulf.
Cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar ta bai wa ƴan ƙasarta da ke zaune a ƙasashen yankin wasu shawarwarin kula da kai da suka haɗa da:
- Kasancewa cikin shiri ta hanyar sanya idanu sosai kan abubuwan da ke faruwa.
- Taƙaita zirga-zirgar da ba ta da muhimmanci sosai.
- Bin umarnin hukumomin ƙasashen da suke ciki.
- Sanin halin da ake ciki ta hanyar bibiyar sahihan kafofin yaɗa labarai.