NE

News Elementor

Sojojin Najeriya Sun Kuɓutar Da Mutum 19 Da aka sace a Abuja

Jami’an tsaron Najeriya sun ce sun kuɓutar da mutum 19 da aka yi garkuwa da su a Abuja, babban birnin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da sojojin ƙasar suka fitar ranar Asabar, sun ce sun kubutar da mutanen a lokacin wani samamen hadin gwiwar jami’an tsaron ƙasar a ƙauyen Gidan Dogo da ke yankin ƙaramar hukumar Bwari.

Sanarwar ta ce jami’an suin kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan maɓoyar ƴanbindigar da suka sace mutanen.

Sojojin sun ce an kashe mutum ɗaya cikin wadanda ake zargi da satar mutanen, yayin da sauran suka gudu, wasu da raunuka.

Satar mutanen domin neman kudin fansa na ci gaba da yawaita a ƴan shekarun nan a Najeriya, inda ƴanbindigar ke far wa garuruwa da tare kan manyan tituna domin satar mutane.

Duk da cewa a baya matsalar ta fi yawa yankin arewa maso yammcin ƙasar, a baya-bayan nan ta yi naso zuwa Abuja, babban birnin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM