NE

News Elementor

Pakistan Ta yi Luguden Wuta Kan Maɓoyar Yanta’adda A Iyakarta Da Afghanistan

Gwamnatin Afghanistan ta ce wasu hare-hare da dakarun Pakistan su ka kai da sanyin safiyar wanan lahadi cikin ƙasar sun kashe gomman mutane da raunata wasu da dama.

Ministan tsaron Pakistan ya faɗa a wanan lahadi cewa an kai hare-haren ne bayan samun bayanai sirri a gameda wuraren da ƴanta’adda suka ɓuya ba tare da yin karin haske ba.

Sai dai a nata bangare gwamnati Afghanistan ta ce harin na Pakistan ya faɗa kan fararen hula ciki har da mata da yara kanana a lardunan Nangarhar da Paktika.

Ba wanan ne karon farko da ake samun dagulewar lamurra a kan iyakar kasashen biyu wato Pakistan da Afghanistan.

Ko a watan octoban shekara 2025 bangarorin biyu sun yi asarar gomman rayuka a wani rikicin da ba’a taɓa ganin irinsa ba da ya ɓarke tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM