NE

News Elementor

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da sace malamai 6 a Zamfara

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da sace wasu malaman addinin Musulunci a Jihar Zamfara, yayin da ta musanta rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da malaman ne a gidan tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari, da ke Talata Mafara, ƙaramar hukumar Talata Mafara.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Rundunar Sojin ta ce an yi garkuwa da waɗanda lamarin ya rutsa da su ne yayin da suke tafiya daga yankin dajin Sububu da ke ƙaramar hukumar Bakura zuwa Talata Mafara.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin, 8 Division, Nigerian Army/Sector 2, Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar mai taken, “Rahoton halin da ake ciki game da sace malaman addinin Musulunci a Jihar Zamfara,” ta bayyana rahotannin cewa an sace malaman ne a gidan Yari a matsayin bayanan da ba su dace da gaskiya ba.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wasu ’yan bindiga da ake zargi ne suka yi garkuwa da limaman Juma’a shida yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar wata addu’a ta musamman da aka shirya domin neman zaman lafiya da kuma nasarar Shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarinsa na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Jaridar ta ruwaito cewa an sace malaman ne kimanin kilomita uku daga ƙauyen Damri, a wani wuri da ake kira Gidan Suleiman Bature da ke dajin Gonar Sarkin.

Shi ma Rundunar ’YanSandan Jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakinta, DSP Yazid Abubakar, ya shaidawa Daily Trust cewa limamai shida ne aka sace.

Rundunar Sojin ta ce dakarunta, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da kuma hanyoyin samun bayanan sirri daga al’ummar yankin, sun ƙara kaimi wajen ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da “labaran da aka yi wa ƙawanya da jan hankali da kuma bayanan da ba a tabbatar da su ba,” waɗanda ka iya haddasa fargaba ko kuma kawo cikas ga ayyukan sojojin da ake gudanarwa a halin yanzu.

Haka kuma, Rundunar ta buƙaci mazauna yankin da su kasance cikin natsuwa da taka-tsantsan, tare da sanar da jami’an tsaro duk wani bayani cikin gaggawa da zai taimaka wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM