
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana matuƙar kaɗuwa, baƙin ciki da kuma damuwa kan mummunan kisan da aka yi wa Shugaban Ƙungiyar Makiyay ta Najeriya MACBAN reshen Jihar Benue, Alhaji Ardo Risku, tare da abokinsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Ba shi shawara kan harkokin yaɗa Labarai, Yomi Odunuga, ya fitar, wadda aka rabawa manema labarai a Makurdi.
A cewar sanarwar, Akume ya bayyana wannan mummunan kisa a matsayin “abin ƙyama, wanda ba za a amince da shi ba, kuma hari ne kai tsaye kan zaman lafiya, sulhu da amincewar juna da al’ummomin Jihar Benue suka yi ta ƙoƙarin sake gina wa cikin wahala.
Ya nuna matuƙar damuwarsa cewa wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da jihar ke ci gaba da samun ingantuwar lamurran tsaro, tare da dawowa da zaman lafiya tsakanin al’ummomin da suke mabanbanta ta fuskar ƙabila, al’ada da addini.
Ya yi gargaɗin cewa ba za a bari maƙiyan zaman lafiya su rushe nasarorin da aka samu ba, waɗanda aka cimma ta hanyar tattaunawa, fahimtar juna da kuma sadaukarwar da kowa ya yi.