Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga al’ummar Hausawa da Fulani da su ƙarfafa dangantaka da fahimtar juna da ke tsakaninsu, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Sarkin Musulmin ya ce bai kamata Hausawa da Fulani su bari a raba kansu ba, yana mai buƙatar su haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, wanda Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Junaid, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a wajen bikin ranar Hausa ta duniya karo na 12 da aka gudanar a Sokoto.
Ya ce yana da muhimmanci ƙabilun biyu, waɗanda ke da alaƙa ta fuskar al’adu da addini, su haɗa kai domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da fahimtar juna.
Sarkin Musulmin ya kuma waiwayi tarihin dangantakar Hausawa da Fulani tun daga zamanin Shehu Usmanu Dan Fodiyo, wanda ya ce ya assasa yanayin haɗin kai da ya ƙarfafa dangantakar addini, kasuwanci da kuma auratayya tsakanin al’ummomin biyu.