Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa Ankara, babban birnin kasar Turkiyya inda zai fara ziyarar aiki ta neman karfafa dangantaka a tsakanin kasashen biyu.
A wani bayani da mai Magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman Ankara, inda ya samu tarba daga ayarin gwamnatin Turkiyya, karkashin jagorancin ministan ilimi na kasar, Yusuf Tekin.
Kazalika, shugaban ya samu tarba daga mai kula da ofishin jekadancin Nigeria a Turkiyya, Ambasada Zayyad Abdulsalam, tare da sauran jami’ai.
Fadar shugaban kasa ta ce ziyarar ta Tinubu za ta mayar da hankali kan inganta dangantaka a tsakanin Nigeria da Turkiyya, da kuma zakulo bangarorin da za su kulla yarjejeniya.
A lokacin ziyarar, shugaba Tinubu zai tattauna da takwaransa na Turkiyya, shugaba Racep Tayyip Erdugan.