NE

News Elementor

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na ƙarfafa shirye-shiryen tallafa wa gidaje masu ƙaramin ƙarfi, domin rage musu raɗaɗin matsin tattalin arziki.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabin bikin cika shekaru 66 da samun yancin kan Najeriya, inda ya amince cewa har yanzu wasu iyalai na fuskantar matsalar samun abinci, biyan kuɗin makaranta da na asibiti, da kuma kuɗin sufuri.

Ya ce matsalolin sun samo asali ne daga ƙarancin samar da kayayyaki, rashin isassun ababen more rayuwa da ƙarancin damar samun ci gaba a tsawon shekaru.

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa na inganta rajistar masu buƙatar tallafi domin tabbatar da cewa tallafin kai tsaye ya isa ga waɗanda suka fi buƙata.

Ya kuma bayyana cewa Asusun Ba da Lamunin Karatu na Najeriya, NELFUND, na taimaka wa ɗaliban da iyalansu ba su da ƙarfin biyan kuɗin karatu, yayin da shirin CreditCo ke ba ’yan Najeriya damar samun rancen sayen muhimman kayayyaki kamar motoci, na’urorin amfani da hasken rana da na’urorin sadarwa.

Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi wajen ƙarfafa kiwon lafiya na matakin farko, ilimin bai ɗaya da sauran muhimman ayyukan gwamnati da talakawa suka dogara da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM