Shugaban Karamar Hukumar Kuje da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, Samuel Danjuma Shekwolo, ya umarci mazauna yankin da ba sa goyon bayan jam’iyyar APC da su bar karamar hukumar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shekwolo ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ya ce ba zai lamunci adawa da APC ko ƙoƙarin sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a cikin karamar hukumar ba.
Shugaban ya ce ya kamata mazauna yankin su goyi bayan jam’iyya mai mulki, duba da ayyukan raya ƙasa da ya ce gwamnatin Tinubu da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, suka aiwatar a Kuje.
Ya ce matsayinsa ba abin tattaunawa ba ne, sannan ya yi alƙawarin yin amfani da ofishinsa wajen adawa da duk wani ƙoƙari na mazauna yankin na yin aiki a kan APC a zaɓen 2027.
Shugaban karamar hukumar ya tambayi dalilin da zai sa mazauna yankin su zaɓi wata jam’iyya da ba APC ba, duk da abin da ya bayyana a matsayin ayyukan tallafi da Tinubu da Wike suka kai wa Kuje.
Kalaman shugaban sun zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara zage damtse wajen shirya gangamin wayar da kan jama’a da kamfen a matakin ƙasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.