NE

News Elementor

Gwamnatin jihar Kano ta ƙara mafi ƙarancin fansho daga N5,000 zuwa N20,000

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara mafi ƙarancin kuɗin fanshon da ake biyan ma’aikatan da suka yi ritaya daga N5,000 zuwa N20,000 a wata.

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Fansho ta Najeriya (NUP), reshen Jihar Kano, Shuaib Musa-Jibrin, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Kano.

Musa-Jibrin ya ce ƙarin kuɗin fanshon ya biyo bayan tattaunawa tsakanin gwamnatin jihar da wakilan ’yan fansho.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Kano ta samu ci gaba wajen biyan basussukan alawus-alawus da sauran hakkokin ’yan fansho.

A cewarsa, daga cikin bashin da aka gada wanda ya kai kusan N48.6 biliyan, gwamnatin ta riga ta biya kusan N32 biliyan, yayin da ake ci gaba da shirin biyan sauran bashin.

Shugaban NUP ɗin ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samu ci gaba wajen biyan fanshon wata-wata a kan lokaci, inda ’yan fansho ke karɓar hakkokinsu tsakanin ranakun 23 zuwa 25 na kowanne wata.

Haka kuma, Musa-Jibrin ya yaba da matakin gwamnatin na dakatar da wasu cire-cire daga fanshon ’yan ritaya, yana mai cewa matakin ya ƙara musu kwarin gwiwa da sauƙaƙa musu rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM