Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, a yayin wata addu’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Ƙasa da ke Abuja domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Tinubu ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su sake ba shi dama a zaɓen 2027 domin ya kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara.
A cewar shugaban, Najeriya ta kai matsayin da ba za a sake kallonta a matsayin ƙasa marar ƙwarewa ba, ganin cewa ta cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Ya ce duk da cewa tafiyar Najeriya tun bayan samun ’yancin kai ta haɗa da nasarori da ƙalubale, akwai damammaki da dama da aka rasa a baya.
“Saƙona ga ƙasa a madadin shugaban ƙasa, shugaban majalisar dattawa da dukkan ’yan majalisar tarayya shi ne kada ’yan ƙasa su yanke ƙauna.
“Zaman lafiya na dawowa ƙasar nan, ci gaba na dawowa, kuma abubuwa za su ƙara inganta yayin da muke ci gaba da dimokuraɗiyya,” in ji shi.
Tinubu ya ce ya kamata ’yan Najeriya su duba manufar gwamnatinsa, musamman yadda take ƙoƙarin gyara “kura-kuran baya da damammakin da aka rasa”.