NE

News Elementor

Wani Ɗalibin Jami’a Ya Kashe Ƙanensa Kan Rikicin Silifas A Jihar Delta

Wani ɗalibi a Jami’ar Federal University of Petroleum Resources da ke Effurun a Jihar Delta ya kashe ƙanensa bayan wata takaddama da ake zargin ta samo asali ne kan silifar banɗaki.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a bayan wani ɗakin kwanan ɗalibai a harabar jami’ar, inda rikicin da ya daɗe tsakanin ’yan uwan biyu ya rikide zuwa faɗa.

Ana zargin babban ɗan uwan ya daba wa ƙanensa wuƙa sau da dama kafin ya tsere daga wurin. Duk da raunin da ya samu, mamacin ya yi ƙoƙarin neman taimako amma daga bisani ya rasu.

Shugaban jami’ar, Farfesa Ezekiel Agbalagba, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rikicin ya faru ne tsakanin ’yan uwa masu uba da uwa ɗaya.

Jami’an tsaro sun fara bincike kan lamarin, yayin da jami’ar ta ce tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da an hukunta wanda ake zargi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM