Rundunar Operation Fansar Yamma da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankin arewa maso yamma, ta ce ta samu nasarar ƙubutar da mutum fiye da 30 da ƴan bindiga suka sace, kuma suke garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi.
Rundunar ta kuma damƙe wasu mutane da take zargin ƴan ta’adda ne.
Sai dai yayin da rundunar ke bayyana waɗannan nasarori, wasu masana harkar tsaro na ganin akwai buƙatar dakarun Najeriyar su kara matsa ƙaimi, wajen bin masu aikata miyagun laifuka har cikin daji, domin su daƙile su.
Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar Aliyu Ɗanja ya aikewa manema labarai, ta ce dakarun rundunar hadin gwiwar sun aiwatar da ayyukan tsaro a jihohin Katsina da Kebbi, a ranakun Litinin da Talata da suka gabata, inda suka kuɓutar da mutum talatin da ɗaya daga hannun ƴan bindiga.
Kana suka ƙwato alburusai da sauran ababen ƙaddamar da hari, da babur, da kayan sarki, da dai sauransu.
Duk da yake dai sanarwar ba ta bayyana yadda lamarin ya kasance ba, ta ce a jihar Katsina, dakarun sun kuɓutar da mutum goma, da suka haɗa da maza uku da mata bakwai, daga hannun ƴan bindiga, bayan samun wani kiran neman ɗaukin gaggawa, game da sace mutanen a ƙauykan Unguwar Daudu da Unguwar Ci-ɓauna na yankin karamar hukumar Funtuwa.
A jihar Kebbi ma, bayan samun wasu ingantattun bayanan sirri, dakarun sun ƙaddamar da wani sintiri irin na fito-na-fito, a ƙauyukan Fafala da Dadikwa na yankin karamar hukumar Kangiwa.