NE

News Elementor

Sojoji sun dakile yunkurin ‘yan ta’adda na kutsawa wasu unguwanni a Borno


Dakarun Operation Hadin Kai sun dakile yunkurin da mayaƙan ISWAP su ka yi na yunkurin kutsawa wasu unguwanni da ke kusa da babban birnin jihar Borno, Maiduguri a safiyar yauJuma’a.

Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Muhammad Goni, ya ce unguwannin da lamarin ya shafa sun haɗa da Muna Garage, Shuwari Village da Ajilari Cross, inda ‘yan ta’addan suka yi ƙoƙarin shiga Maiduguri tsakanin ƙarfe 12:20 na dare zuwa 2:30 na safe.

Ya bayyana cewa dakarun sun gano motsin maharan tun da wuri, inda su ka buɗe musu wuta daga wurare daban-daban, lamarin da ya tilasta su ka tsere.

Haka kuma, ina ji Goni, sojojin sun dakile wani yunkuri na yan ta’addan na kutsawa yankunan Miringa da Dutsen Kura da ke Buratai.
Goni ya ce a halin yanzu dakarun na ci gaba da gudanar da sintiri da bincike domin bibiyar maharan da suka tsere tare da tabbatar da tsaron al’ummomin yankin.

Ya kuma bukaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin tallafa wa yaƙi da ta’addanci a Arewa maso Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM