NE

News Elementor

Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro yayin da gwamnatin tarayya ke nazari kan tsanantar matsalar tsaro a Nigeria

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gudanar da wata ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da Gwamnatin Tarayya ke nazari kan tabarɓarewar matsalar tsaro a sassan ƙasar nan.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan cikakken nazarin ƙalubalen tsaro da kuma abubuwan da ke faruwa a wuraren da jami’an tsaro ke gudanar da ayyuka.

Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Christopher Musa; Hafsan Sojin Ƙasa, Olufemi Oluyede; da Shugaban Hukumar Leken Asirin Sojoji, Emmanuel Undiandeye.

Haka kuma akwai Darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya (DSS), Adeola Ajayi da Darakta Janar na hukumar leken asiri ta ƙasa (NIA), Mohammed Mohammed; Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaron Cikin Gida, Manjo Janar Adeyinka Famadewa mai ritaya; da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunde Disu, tare da sauran manyan jami’an tsaro.

Ganawar ta gudana ne sa’o’i 48 bayan dakarun Operation FANSAN YAMMA tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Sama ta Joint Task Force ta Arewa maso Yamma sun dakile wani hari da sojoji suka ce ‘yan ta’adda suka shirya kai wa a jihohin Zamfara da Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM