
Tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, da jam’iyyarsa suna hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu samun nutsuwar barci.
Tambuwal ya yi zargin cewa Tinubu da jam’iyyar APC suna kitsa wasu tsare-tsare domin dakile ci gaban ADC, amma Allah na rusa waɗannan shirye-shirye.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓa tsohon shugaban ƙaramar hukumar Tangaza, Isa Salihu Bashir Kalanjeni, zuwa jam’iyyar ADC bayan ya fice daga APC.
A yayin taron, Tambuwal ya bayyana Tinubu a matsayin shugaban ƙasa mai shirin barin mulki.Tambuwal ya ƙara da cewa wasu ‘yan siyasa da dama sun yi jinkirin shiga ADC saboda tsoron matsin lamba da ka iya biyo bayan ficewa daga jam’iyya mai mulki.