NE

News Elementor

Tinubu ya amince da faɗaɗa Rundunar Sojin Najeriya zuwa rundunoni 12 tare da daukar sabbin sojoji dubu 28

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da faɗaɗa tsarin Rundunar Sojin Najeriya daga rundunoni takwas zuwa 12 tare da ɗaukar sabbin sojoji 28,000 domin ƙarfafa tsaron ƙasa.

Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa Shawara kan yaɗa labarai , Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce matakin zai inganta jagoranci da gudanar da ayyukan soja, ƙarfafa tsaron kan iyakoki, kare muhimman ababen more rayuwa, da kuma haɓaka yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.

Sabbin rundunonin za su kasance a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin City, yayin da za a aiwatar da sabon tsarin kashi biyu.

Kashi na farko zai kammala nan da watan Satumban 2026, yayin da na biyu zai kammala zuwa watan Disamban 2026.

Shugaba Tinubu ya kuma yabawa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Ibrahim Shuaibu, da dakarun rundunar bisa jajircewarsu wajen kare haɗin kan Najeriya da tsaron ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM