
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nanata kudurin gwamnatinsa wajan samar da hadin-kai, zaman lafiya da kuma hakuri da juna a tsakanin mabiya addinai a Nigeria.
Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin ministan harkokin wajen fadar Vatican, Archbishop Paul R. Gallagher, a gidansa dake birnin Abuja.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya ce samun daidaito a tsakanin mabiya addinai, shi ne kadai hanyar da za a bi wajan magance kalubalen tsaro a kasar nan.
Ya shedawa babban limamin chochin na katolika cewa, yana da kyakkyawar alaka da wannan chochin, musamman lokacin da yake gwamnan Legas, inda ya bayyana goyon bayansa ga shirye-shiryen da chochin ke yi a bangaren ilimi da kiwon lafiya.
Shugaban kasa ya ce wannan imanin ne ya sa ya yi kokarin farfado da makarantun mission a lokacin da ya zama gwamna, wadanda gwamnatocin baya na mulkin soji suka kwace.