NE

News Elementor

Tinubu ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a haɗarin jirgin ruwa a Sokoto

Shugaban kasa Bola Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin jirgin ruwa na Gorau, dake cikin karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, wanda ya yi nasadin mutuwa da batan mutane da dama.

Ya bayyana hadarin a matsayin kaddara, tare da jajantawa gwamnati da alummar jihar Sokoto kan wannan lamarin.

A wani bayani da mai Magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban kasa ya ce ya kadu matuka da jin labarin hadarin jirgin.

Ya isar da sakon fatan alkairi da adduoi kan iyalan wadanda lamarin ya shafa, tare da rokon Allah ya jikansu da rahama ya kuma bawa yan uwansu hakurin jure wannan rashi.

Tinubu ya kuma yabawa masu bada agaji da hukumomin yankin kan daukin da suka kai cikin gaggawa.

Daga nan ya umarci hukumomin da lamarin ya shafa, kamar NIWA da NEMA da su yi aiki tare da gwamnatin jihar Sokoto domin kare aukuwar hakan a nan gaba, da kuma tabbatar da cewa mutane na yin biyayya ga dokokin sufurin ruwa a Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM