NE

News Elementor

Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da masallata a jihar Neja

Rahotanni daga Jihar Neja na cewa wasu ’yan bindiga sun kai hare-hare kan wasu al’ummomi a ƙaramar hukumar Borgu, inda suka yi garkuwa da wasu masu ibada jim kaɗan bayan sallar Juma’a.

An ce hare-haren sun faru ne a Dekara, Gidan Zana, Sabon Gida da Masaka, kamar yadda mazauna yankin da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Jafar Muhammad Shetiman Borgu, suka bayyana.

Ɗan majalisar ya ce har yanzu ba a san ainihin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, amma ya tabbatar da cewa wasu masu ibada sun samu raunuka bayan an kai musu hari da adduna.

Ya ce maharan sun shiga Dekara ne bayan sallar Juma’a, inda suka kewaye wani masallaci tare da tafi da masu ibadar zuwa cikin daji. Daga nan kuma suka shiga wasu garuruwan da ke makwabtaka da yankin, inda suka sake yin garkuwa da wasu mutane.

Rahotanni sun ce matasa da magidanta na cikin waɗanda aka yi garkuwa da su. Yankin Borgu na da iyaka da jihohin Kebbi da Kwara, da kuma Jamhuriyar Benin, abin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a kan matsalar tsaro a yankin.

Shetiman Borgu ya ce dazuzzukan yankin sun zama maboyar wasu da ake zargin ’yan ƙungiyoyin Lakurawa da Mamudawa ne. Ya kuma ce an samu rashin jituwa tsakanin ƙungiyoyin biyu bayan harin, inda wasu daga cikinsu suka nuna adawa da kai hari kan masallatai da yin garkuwa da masu ibada.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko waɗanda suka kai harin na cikin Lakurawa ko Mamudawa ba. Hukumomi na zargin cewa maharan na iya kasancewa suna neman matasa ne domin ɗaukar su cikin ƙungiyoyin.

Hare-haren sun ƙara jaddada matsalar tsaro da al’ummomin Borgu ke fuskanta. A makon da ya gabata ma, an bayar da rahoton kashe mutane sama da 20 a wasu sassan ƙaramar hukumar, yayin da a watan Nuwamban 2025 aka yi garkuwa da ɗalibai sama da 200 a Papiri, daga bisani aka sake su bayan kusan wata guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM