NE

News Elementor

Tinubu Ya Nemi Majalisa Da Amince Domin Naɗa Wanda Zai Maye Gurbin Shugaban Hukumar NMDPRA Da Ya Aje Aiki

Shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa, Injiniya Farouk Ahmed da takwaransa Gbenga Komolafe sun ajiye aikinsu, kuma tuni da shugaban ƙasa, Shugaba Tinubu ya miƙa sunayen waɗanda za su gaje su ga Majalisar Dattawa domin amincewa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sababbin manyan daraktoci biyu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar a da yammacin wannan Larba.

Onanuga ya ce Bukatar ta biyo bayan murabus ɗin Injiniya Farouk Ahmed na hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA da Gbenga Komolafe na NUPRC.

Dukkanin jami’an biyu tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ne ya naɗa su a shekarar 2021 domin jagorantar hukumomin da Dokar Masana’antar Man Fetur ta kafa.

Domin cike guraben, Shugaba Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattawa wasiƙa, inda ya nemi ta hanzarta tantancewa da amincewa da Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin Babbar Darakta ta hukumar NUPRC, da kuma Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin Babban Daraktan Hukumar kula da man fetur ta ƙasa NMDPRA.

Mutanen biyu ƙwararrun masana ne da suka daɗe suna aiki a fannin mai da iskar gas.

Eyesan, wadda ta kammala karatu a fannin Tattalin Arziki a Jami’ar Benin, ta shafe kusan shekaru 33 tana aiki a NNPC da rassan kamfanin.

Ta yi ritaya a matsayin Mataimakiyar Shugaban Zartarwa a hukumar kula da raba mai daga (2023–2024), sannan a baya ta riƙe muƙamin Babbar Manaja ta Tsare-tsare da Dabaru a NNPC daga 2019 zuwa 2023.

Injiniya Saidu Aliyu Mohammed kuwa, wanda aka haifa a shekarar 1957 a Jihar Gombe, ya kammala karatu a Jami’ar Ahmadu Bello a 1981 inda ya samu digirin farko a fannin Chemical Engineering.

Kuma a yanzu an sanar da sunansa a matsayin wanda zai maye gurbin Eng Farouk Ahmad.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM