Wani mazaunin jihar Filato mai bin addinin Kiristanci, Peter Ibrahim Gyendyeng, ya gina masallacin Juma’a ga al’ummar Musulmi da ke garin Gana Ropp a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato.
Gina wannan masallaci ya sanya farin ciki sosai ga al’ummar Musulmi a yankin, waɗanda suka bayyana wannan mataki a matsayin wata alama ta tabbatar da zaman lafiya da nuna ƙauna a tsakanin al’umma.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da wasu sassan jihar ta Filato, ciki har da ƙaramar hukumar Barkin Ladi, ke fuskantar ƙalubalen tsaro da rikice-rikice da suka shafi dangantaka tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristanci a ‘yan kwanakin nan.
Da yake jawabi yayin buɗe masallacin, Gyendyeng, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Barkin Ladi/Bassa, ya bayyana cewa ya gina wurin ibadar ne domin ya zama wata alama ta haɗin kai da zaman tare tsakanin mabiya addinin Kirista da Musulmi a yankin da ma jihar baki ɗaya.
Gyendyeng ya bayyana cewa duk kuɗin da za a ba al’umma ƙarewa za su yi cikin ƙanƙanin lokaci, amma gina musu wurin ibada da za su riƙa yin addu’ar zaman lafiya da ci gaban ƙasa abu ne mai ɗorewa, yana mai ƙara da cewa hanya mafi kyau ta taimaka wa mutane ita ce ba su abin da suke matuƙar ƙauna.
Da yake mayar da jawabi, babban limamin masallacin, Sheikh Ladan Gana Ropp, ya bayyana cewa al’ummar Musulmi sun yi matuƙar farin ciki da wannan aiki wanda ya ba su damar samun ‘yanci da kwanciyar hankali a garin.
Babban limamin ya kuma yi kira ga mabiya addinin Kirista da na Musulunci a yankin da jihar Filato baki ɗaya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai, da juna domin ci gaban ɗan adam.
Jariday Daily Trust ta ruwaito cewa, a wajen buɗe masallacin dai ya samu halartar fastoci, shugabannin coci, da sauran al’ummar Kirista na yankin.