‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum tara, sun harbe wani mutum guda tare da kwashe dabbobi sama da 200 a lokacin da suka kai hari a kauyen Illelar Dawagari da ke Unguwar Kagara, ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin yankin da ya zanta da Daily Trust ya ce maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren Asabar.
Mazaunin ya ce ɗaya daga cikin mutanen da aka harba, mai suna Saminu Arzika, ya fita domin yin bayan gida, inda ya lura da alamun‘yan bindigar.
Ya ce Arzika ya haska musu fitila, inda ya ga ‘yan bindigar, sannan lokacin da ya sake ƙoƙarin haska musu fitilar, sai suka umarci a harbe shi.
A cewarsa, Arzika ya gudu zuwa cikin gari, amma ‘yan bindigar suka bi shi tare da harbe shi, inda karar harbin bindigar ta sanar da mazauna yankin abin da ke faruwa, lamarin da ya sa suka gudu zuwa dajin da ke kusa domin tsira.
Mazaunin ya ce shi ma ya gama cin abinci a gida ne sannan ya fita domin sayen magani.
Ya ce bayan ya bar shagon, sai ya nufi wani shago domin sayen kwalbar lemo, inda ya ji karar harbin bindiga.
Ya ce nan take ya fara gudu domin tsira, inda ya rika tsallake katangar gidaje har sai da ya tsere zuwa cikin daji.
Mazaunin ya ce ‘yan bindigar sun ci gaba da gudanar da farmakin har zuwa misalin ƙarfe 11 na dare, inda suka rika shiga gidaje ɗaya bayan ɗaya tare da kwashe dabbobi da aka kiyasta yawansu ya haura 200.
Ya ce maharan sun kuma yi garkuwa da mutane tara, waɗanda suka ƙunshi maza biyar da mata huɗu.
Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, ya ce akwai Maryam Yusuf, Rukayya Abdu da wata gwauruwa mai suna Maryam Abdullahi, yayin da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su yara ne ‘yan tsakanin shekara 10 zuwa 15, waɗanda bai iya gano sunayensu ba.