NE

News Elementor

Wani matashi ɗan Najeriya, Samuel Ezekiel, ya bayyana yadda wani abokinsa ya yaudare shi har aka cire masa ƙoda a wani asibiti da ke Abuja.

Ezekiel ya ce abokinsa mai suna Emmanuel Odeh ne ya kai shi asibiti, bayan ya tabbatar masa cewa za su je ne domin wani abu da bai bayyana masa ba. Ya ce saboda amincewarsa da abokin nasa, ya bi umarninsa ba tare da zargi ba.

A cewarsa, daga baya Odeh ya haɗa shi da wani mutum mai suna David, wanda ya kai shi wurin wani dillali mai suna Ben domin gudanar da gwaje-gwajen lafiya.

Ezekiel ya ce bayan sakamakon gwajin farko bai yi daidai da na wanda aka shirya bai wa ƙodar ba, sai aka sanar da su cewa an samu wani mutum daban da ƙodarsa ta yi daidai da tasa.

Ya ce daga nan aka sanar da shi cewa za a sauya sunansa zuwa Hassan Abubakar, kafin a kai shi Babbar Kotun Tarayya domin shirya masa takardar rantsuwa.

Bayan kammala wannan mataki ne aka kai shi Wellington Hospital da ke Life Camp, Abuja, inda aka sa shi ya sanya hannu kan wasu takardu kafin a kai shi ɗakin tiyata domin cire ƙodar.

Matashin ya ce kafin ya shiga ɗakin tiyatar, da misalin ƙarfe 10 zuwa 11 na dare, aka kawo musu kuɗin da aka biya domin ƙodar, wanda ya ce an bayar da shi ne cikin daloli.

Ya ce saboda amincewarsa da abokinsa, sai ya ba Emmanuel kuɗin ya riƙe masa.

Sai dai Ezekiel ya ce bayan da aka yi masa tiyatar, ya gano cewa abokin nasa ya riga ya canza kuɗin tare da kashe wani ɓangare daga ciki wajen sayen kayayyakin lantarki.

Ya ce Emmanuel ya sayi wayoyi biyu, power bank guda biyu da na’urorin Wi-Fi guda biyu, inda ya ba shi ɗaya daga kowanne, sannan ya riƙe ɗayan.

Ezekiel ya ce sun kwashe kusan mako guda a asibiti kafin a sallame su, daga nan kuma Emmanuel ya kai shi wani otal inda suka kwashe wasu kwanaki biyu.

Matashin ya bayyana hakan ne yayin da rundunar ’yan sandan Najeriya ta gabatar da wasu waɗanda ake zargi da hannu a wata ƙungiyar safarar gabobi a Abuja da jihar Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM